DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Jam’iyyar APC na neman gwamnatin tarayya ta kafa dokar ta-baci a jihar Rivers

-

Shugabancin jam’iyyar APC a jihar Rivers ya roki gwamnatin tarayya da ta kafa dokar ta-baci a jihar.
Shugaban rikon jam’iyyar a jihar Mr Tony Okocha ne ya yi wannan rokon a lokacin wani taron manema labarai a Fatakwal babban birnin jihar.
Ya ce jihar Rivers na cikin halin yakin da ya lakume rayukan mutanen da ba a san adadinsu ba ya zuwa yanzu.
Gwamnatin tarayya dai na da hurumin kakaba dokar ta-baci a duk jihar da aka samu barkewar wata annoba, rikicin da ya ki ci, ya ki cinyewa, zazzafan fadan da ya ki karewa a tsakanin bangarori, barkewar wata cuta ko wasu abubuwan da ke kawo barazana ga tsaro.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

INEC za ta fara sabuwar rijistar katin zaɓe daga ranar 18 ga Agusta a Nijeriya

Hukumar Zaɓen Nijeriya INEC ta sanar da ranar 18 ga watan Agusta, 2025 a matsayin ranar da za ta fara sabuwar rijistar katin zaɓe a...

Kamfanin NNPCL ya musanta labarin cefanar da matatar man birnin Port Harcourt

Kamfanin man fetur na Nijeriya NNPCL ya musanta labarin cefanar da matatar mai ta Fatakwal ga yan kasuwa A Yayin wani taro da kamfanin ya gabatar...

Mafi Shahara