DCL Hausa Radio
Kaitsaye

‘Yan bindiga sun sake shiga garin Dutsinma jihar Katsina, sun aike da malamin jami’ar FUDMA lahira

-

Wasu ‘yan bindiga da ba a kai ga tantance adadinsu ba ya zuwa wannan lokaci sun kutsa kai cikin garin Dutsinma na jihar Katsina, inda suka harbe wani malamin jami’ar tarayya ta FUDMA da aka bayyana sunansa da Dr Tiri.
Majiyar DCL Hausa ta kuma ce maharan sun kuma yi awon-gaba da ‘ya’yansa biyu da ba a sanar da jinsinsu ba, wato maza ne ko mata, ko kuma mace da namiji.
Lamarin ya faru a daren Litinin wayewar Talata da misalin karfe 1am.
Majiyar ta ce yanzu haka gawar Dr Tiri da ke koyarwa a sashen tattalin arziki na fannin noma na can a babban asibitin garin Dutsinma jihar Katsina.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ASP Aliyu Abubakar Sadiq bai kai ga amsa kiran wayar da DCL Hausa ta yi masa ba kan lamarin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Yan kasuwar mai sun sauke farashin man fetur kasa da yadda Dagote ke sayarwa

Wasu masu shigo da man fetur daga ƙasashen waje sun fara sayar da shi a ƙasa da Naira 860 kowace lita, lamarin da ya sauka...

Saurayi ya gaggabe wa budurwarsa hakora shida a Legas

Wani saurayi a unguwar Ibadan dake Ebute Meta, jihar Legas, ya lakadawa budurwarsa Fatima, wadda ke sana’ar gyaran kai, dukan da ya janyo ta rasa...

Mafi Shahara