DCL Hausa Radio
Kaitsaye

An kafa cibiyoyin samar da lantarki a wasu manyan jami’o’in Nijeriya, in ji ministan makamashi

-

Gwamnatin tarayya ta hanyar hukumar wutar lantarki sanya cibiyar samar da lantarki a manyan jami’o’i shida na tarayya, a matsayin wani yunkuri na samar da ingantacciyar wutar lantarki a muhimman bangarori ga al’umma.
Hukumar ta bayyana cewa ta samu gagarumin ci gaba wajen bunkasa ayyukan samar da wutar lantarki a Najeriya.
Wannan ya biyo bayan wata tattaunawa da daraktan hukumar, Abba Abubakar Aliyu, ya yi da ministan kudi kuma ministan tsare-tsare na tattalin arziki, Wale Edun.
Jami’o’in sun hada da jami’ar Abuja, jami’ar Maiduguri, jami’ar koyon dabarun aikin gona ta Michael Okpara da ke Umudike, jami’ar tarayya ta Gashua a Yobe, jami’ar ta tarayya da ke Abeokuta, da kuma kwalejin tsaro ta Najeriya da ke Kaduna.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Tarihin marigayi Aminu Dantata

Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un. Najeriya ta yi babban rashi – na dattijo, attajiri, mai hangen nesa da zuciya mai tausayi: Alhaji Aminu Alhassan...

Bayan shafe watanni 23, Ganduje ya ajiye mukamin shugabancin APC

Ta dai tabbata, Abdullahi Umar Ganduje ya yi murabus daga shugabancin jam'iyyar APC ta kasa. Tsohon Gwamnan jihar Kanon ya ajiye mukamin nasa da yammacin Juma'ar...

Mafi Shahara