DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Kafa hukumar kula da Almajirai zai inganta karatun allo a Nijeriya – Sarkin Musulmi

-

Mai Alfarma Sarkin Muslimi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar ya bayyana cewa Shugaban Hukumar Ilimin Almajirai da Yaran da Ba sa zuwa Makaranta,

Dr Muhammad Sani Idris, mutum ne da ke da kwarewa a kan yadda za a magance matsalolin da suka addabi karatun allo da yaran da ba sa zuwa makaranta.
Sarkin Musilmin ya na magana ne yayin da wata tawaga daga hukumar ta ziyarce shi a fadarsa dake Sokoto.
Ya kuma tabbatar da goyon bayansa ga kudirin hukumar na magance wadannan matsaloli inda ya ce zai tattauna da sarakuna gatgajiya domin samun goyon bayansu. 
Tun da farko,Shugaban Hukumar Almajirai da Yaran da Ba Sa Zuwa Makaranta, Dr Muhammad Sani Idris ya ce twawagar ta sa, ta ziyarci Mai Marataba Sarkin Musulmi ne domin ya sa wa hukumar albarka a wannan aiki na gyara karatun allo, dakuma sa, ko mayar da yara makaranta, tare da koya musu sama’o’i domin dogaro da kai.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Bayan shafe watanni 23, Ganduje ya ajiye mukamin shugabancin APC

Ta dai tabbata, Abdullahi Umar Ganduje ya yi murabus daga shugabancin jam'iyyar APC ta kasa. Tsohon Gwamnan jihar Kanon ya ajiye mukamin nasa da yammacin Juma'ar...

Indomie ta kaddamar da gangami don tallafa wa nasarar iyaye da ‘ya’ƴansu

Indomie, shahararren kamfanin taliyar Indomie a Najeriya, ya ƙaddamar da sabon gangami mai taken “Ingantaccen Abinci Domin Nasara”. Wannan gangami yana jaddada muhimmancin abinci mai...

Mafi Shahara