DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Zanga-zangar rashin Sarkin Gobir, ta sa gwamnatin jihar Sokoto kakaba dokar hana fita

-

Rundunar ‘yan sandan jihar Sokoto ta tabbatar da kafa dokar hana fita a karamar hukumar Sabon Birni a jihar, bayan da matasa suka tayar da tarzoma kan kashe sarkin Gobir, Isa Muhammad Bawa.
Kakakin rundunar, ASP Ahmed Rufa’i, ya ce ba za a yarda da wani motsi a yankin daga karfe 6 na safe zuwa karfe 6 na yamma ba har sai an samu sanarwar da ta sauya hakan.
Ya ce an dauki wannan matakin ne don dawo da doka da oda a yankin.
Daruruwan matasa sun cika wasu manyan hanyoyin yankin tare da kunna wuta a manyan tituna.
 An kuma ce matasan sun banka wa sakatariyar jam’iyyar APC ta karamar hukumar wuta tare da kone wata kotu.
Haka kuma sun balle wani rumbun ajiya na gwamnati na karamar hukumar inda suka lalata takin zamani.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Mijina (Sani Abacha) bai saci kudin Najeriya ba -Maryam Abacha

Tsohuwar matar shugaban kasa, Maryam Abacha, ta musanta zargin cewa marigayi mijinta, Janar Sani Abacha, ya wawure dukiyar kasa. A wata hira da aka watsa a...

‘Yan sanda a Katsina sun ceto mutane 11 da aka yi yunkurin garkuwa da su

Hadakar 'yan sanda, jami'an tsaron sirri na DSS, sojoji da jami'an C-Watch hade da 'yan banga a jihar Katsina sun yi nasarar kubutar da mutane...

Mafi Shahara