DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Hisbah a Kano na tsare da kwamishina daga jihar Jigawa bisa zarginsa da lalata da matar aure

-

Jami’an hukumar Hisbah a jihar Kano sun kama kwamishinan ayyuka na musamman na jihar Jigawa Awwal Danladi Sankara bisa zargin lalata da matar aure.

Jaridar Daily Nigerian ta rawaito cewa jami’an na Hisbah sun kama wanda ake zargin bayan da suka samu korafi daga mijin matar, da ya ce yana zargin akwai kullalliya tsakanin kwamishinan da matarsa.
Bayanai sun ce har yanzu ana tsare da wannan kwamishina a hukumar Hisbah ta Kano.
Mijin matar, ya ce suna da ‘ya’ya biyu da su ma ya diga ayar tambaya a kansu.
Hukumar Hisbah ta ce ta kama wanda ake zargin ne da misalin karfe 10 na daren Alhamis tare da matar a lokacin da suke kokarin shiga wani kango mallakin kwamishinan.
Hisbah ta ce a lokacin da aka isa da su hedikwatarta, wanda ake zargin ya amsa cewa ya taba kwanciya da matar sau uku kacal.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Akwai tabbaci kan zargin kaso 80% na rashawa a Nijeriya – ICPC

Hukumar ICPC ta bayyana cewa matsalar rashawa a Najeriya ta yi zurfi matuka, inda ta ce idan aka aiwatar da dokoki yadda ya kamata, kusan...

Gwamnatin Tinubu na tuhumar Stella Oduah, da cin hancin ₦5bn

Tsohuwar Ministar Sufurin Jiragen Saman Nijeriya, Stella Oduah, ta gurfanar a gaban kotu Abuja ranar Laraba kan zargin cin hanci da rashawa na biliyan 5 An...

Mafi Shahara