DCL Hausa Radio
Kaitsaye

MƊD ta Jajanta wa Nijeriya kan fashewar tankar mai a Jigawa

-

Wakilin Babban Sakataren Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya na musamman mai kula da yammacin Afirka da yankin Sahel, Leonardo Santos Simão, ya bayyana matukar bakin cikinsa dangane da mummunan fashewar wata tankar man fetur a garin Majiya da ke ƙaramar hukumar Taura a Jihar Jigawa.
A cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar 17 ga watan Oktoba, Simão ya mika ta’aziyyarsa ga iyalan wadanda abin ya shafa, da kuma gwamnati da al’ummar Najeriya.
Fashewar wadda ta afku cikin muni ta yi sanadiyar mutuwar mutane sama da 150 tare da jikkata wasu da dama, lamarin da ya yi matukar barna.
Simão ya kuma yi fatan samun sauki cikin gaggawa ga wadanda bala’in ya shafa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Mun raba Naira biliyan 116.4 ga ɗalibai sama da dubu 624 – Asusun NELFUND

Asusun ba da bashin karatu ga ɗaliban manyan makarantu ya bayyana cewa ya raba Naira biliyan 116.4 ga ɗalibai sama da dubu 624, tun bayan...

Tsohon kwamishinan Ganduje ya soki gwamnatin Abba bisa zargin sayar da filin makarantar

Tsohon kwamishinan ilimi na a zamanin Ganduje, Muhammad Sanusi Sa'id Kiru, ya soki matakin gwamnatin Abba Kabir Yusuf na mayar da Makarantar Sakandare ta ‘Yan...

Mafi Shahara