DCL Hausa Radio
Kaitsaye

MƊD ta Jajanta wa Nijeriya kan fashewar tankar mai a Jigawa

-

Wakilin Babban Sakataren Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya na musamman mai kula da yammacin Afirka da yankin Sahel, Leonardo Santos Simão, ya bayyana matukar bakin cikinsa dangane da mummunan fashewar wata tankar man fetur a garin Majiya da ke ƙaramar hukumar Taura a Jihar Jigawa.
A cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar 17 ga watan Oktoba, Simão ya mika ta’aziyyarsa ga iyalan wadanda abin ya shafa, da kuma gwamnati da al’ummar Najeriya.
Fashewar wadda ta afku cikin muni ta yi sanadiyar mutuwar mutane sama da 150 tare da jikkata wasu da dama, lamarin da ya yi matukar barna.
Simão ya kuma yi fatan samun sauki cikin gaggawa ga wadanda bala’in ya shafa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Shugaba Bola Ahmad Tinubu ya yi ganawar sirri da sabbin hafsoshin tsaro a Abuja

Taron, wanda ya gudana kwanaki uku bayan sanar da sabbin nade-naden, shi ne karo na farko da shugaban kasa ya gana da manyan hafsoshin rundunonin...

Paul Biya ya yi wa masu zanga-zangar sakamakon zabe shagube a Kamaru

Shugaban ƙasar Kamaru, Paul Biya, ya yi shagube ga rikicin siyasar da ke faruwa bayan ayyana shi a matsayin wanda ya lashe sakamakon zaɓen shugaban...

Mafi Shahara