DCL Hausa Radio
Kaitsaye

MƊD ta Jajanta wa Nijeriya kan fashewar tankar mai a Jigawa

-

Wakilin Babban Sakataren Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya na musamman mai kula da yammacin Afirka da yankin Sahel, Leonardo Santos Simão, ya bayyana matukar bakin cikinsa dangane da mummunan fashewar wata tankar man fetur a garin Majiya da ke ƙaramar hukumar Taura a Jihar Jigawa.
A cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar 17 ga watan Oktoba, Simão ya mika ta’aziyyarsa ga iyalan wadanda abin ya shafa, da kuma gwamnati da al’ummar Najeriya.
Fashewar wadda ta afku cikin muni ta yi sanadiyar mutuwar mutane sama da 150 tare da jikkata wasu da dama, lamarin da ya yi matukar barna.
Simão ya kuma yi fatan samun sauki cikin gaggawa ga wadanda bala’in ya shafa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Hukumar tace fina-finai ta Kano ta soke lasisin wani gidan gala bisa dalilai na tsaro

Hukumar Tace Fina-finai ta Jihar Kano ta soke lasisin gudanar da ayyukan wani gidan gala mai suna Sunsiro Entertainment, wanda ke kan titin Yahaya Gusau,...

Dimukuradiyyar Nijeriya na cikin barazana a mulkin Tinubu – Atiku Abubakar

Tsohon mataimakin shugaban Nijeriya Atiku Abubakar ya nuna damuwa kan karancin fitowar masu kada kuri'a a zaben da aka gudanar ranar Asabar a Abuja. Cikin wani...

Mafi Shahara