DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Barayin daji sun yi ajalin mutane a Jibia jihar Katsina

-

‘Yan ta’adda sun kai hari a Umguwar Bachaka cikin garin Jibia na jihar Katsina, inda suka kashe mutane 3 suka kuma sace da dama.
Wata majiya daga garin na Jibia da ta nemi kada a ambaci sunanta ta shaida wa DCL Hausa cewa maharan sun shiga garin ne da misalin karfe 11 na daren Asabar, suka fara harbin kan mai uwa da wabi da hakan ya jefa al’ummar yankin cikin razani.
Majiyar ta ce barayi sun rika bi gida-gida a cikin unguwar, inda suka ji wa karin wasu raunuka mafi yawansu kananan yara.
Har zuwa safiyar Lahadin nan dai, majiyar ta ce ba a iya tantance yawan mutanen da barayin dajin suka sace ba a Umguwar ta Bachaka da ke tsakiyar garin na Jibia.
Hukumomi a jihar Katsina ba su ce uffan ba game da batun.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Nijeriya za ta rika ba wa kasashe bashin kudi nan da 2026 – Oluremi Tinubu

Uwargidan shugaban Nijeriya Sanata Oluremi Tinubu ta ce nan da shekarar 2026 Nijeriya za ta rika ba wa wasu kasashen bashin kudade.   Oluremi ta bayyana haka...

An kaddamar da kafar yaɗa labarai ta Hausa don mata zalla a Nijeriya

An kaddamar da Mata Media, kafar yaɗa labarai ta farko a Nijeriya da aka ware musamman domin mata, wacce ke aikin shirya labarai na abubuwan...

Mafi Shahara