DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Kungiyar likitoci ta ba gwamnatin Abba Gida-Gida sa’o’i 48 kan zargin cin zarafin likita

-

Kungiyar likitocin Nijeriya reshen jihar Kano, ta ba da wa’adi ga gwamnatin jihar da ta gaggauta korar kwamishiniyar jin kai, Amina Abdullahi, sakamakon cin zarafin wata likita.

A wata sanarwa da shugaban Kungiyar, Dr. Abdurrahman Ali da Sakatare, Dr. Ibrahim D. Muhammad suka sanya wa hannu, kungiyar ta bayyana cewa lamarin ya faru ne a ranar 1 ga watan Nuwamba a sashin kula da kananan yara na asibitin kwararru na Murtala Muhammad.

A cewar sanarwar, an yi zargin Kwamishinar da mukarrabanta da jami’an tsaro suka ci zarafin likitar. 

Zargin cin zarafin dai ya samo asali ne sakamakon rashin samun magungunan da aka rubuta wa marasa lafiya, yayin da ta ke kula da marasa lafiya sama da 100.

Biyo bayan wannan al’amari, kungiyar Kano ta yi barazanar dakatar da aikin jinya a asibitin kwararru na Murtala Muhammad cikin sa’o’i 48, idan ba a biya musu bukatunsu ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

An saka ranar da za a fitar da sakamakon binciken zargin alaka da muggan kwayoyi da ya hada da Shugaba Tinubu na Nijeriya

An saka ranar da za a fitar da sakamakon binciken zargin alaka da muggan kwayoyi da ya hada da Shugaba Tinubu na Nijeriya. Ana dai...

Za mu iya cin zabenmu ko babu ku, kalaman Elrufa’i ga gwamnonin Nijeriya

  Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya bayyana cewa sabuwar kawancen jam’iyyu adawa na da karfin da zai kayar da Shugaba Bola Ahmed Tinubu...

Mafi Shahara