DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Hedikwatar tsaron Nijeriya na neman karin wasu ‘yan ta’adda ruwa jallo

-

Mutanen da ake nema ruwa a jallo sun hada da Abu Khadijah, Abdurrahman, Dadi Gumba, Abu Muhammed, Usman Kanin Shehu, Abu Yusuf, Musa Wa’a, Ibrahim Suyeka, BA Sulhu da Idris Taklakse.

Google search engine

Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da babban hafsan sojin kasar ya tabbatar da bullar wata sabuwar kungiyar ta’addanci da aka fi sani da ‘Lukarawas,’ wanda ke kara ta’azzara matsalar rashin tsaro a yankin arewa maso yammacin Nijeriya.

Daraktan yada labaran hedikwatar tsaro, Maj Janar Edward Buba, ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai kan ayyukan rundunar a ranar Alhamis a Abuja.

Ya ce sabuwar kungiyar ta’addancin ta bulla ne daga Jamhuriyar Nijar bayan juyin mulkin da ya kai ga rugujewar hadin gwiwar sojoji tsakanin Nijeriya da Nijar din.

Ya kara da cewa ‘yan ta’addan sun fara kutsawa cikin yankunan arewacin jihohin Sokoto da Kebbi daga jamhuriyar Nijar da Mali, musamman bayan juyin mulkin da aka yi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

PDP ta ce za ta daukaka kara kan hukuncin dakatar da babban taronta a Ibadan

Jam’iyyar PDP ta ce za ta daukaka kara kan hukuncin kotun tarayya da ta dakatar da gudanar da babban taronta da aka shirya yi a...

Matatar man Dangote ta yi alkawarin samar da wadataccen man fetur a lokacin bukukuwan karshen shekara

Matatar man Dangote ta tabbatar da cewa za ta samar da isasshen man fetur da dizal a fadin Nijeriya a lokacin bukukuwan karshen shekara domin...

Mafi Shahara