DCL Hausa Radio
Kaitsaye

‘Yan bindiga sun yi barna a Kaduna

-

Gwamnan Kaduna Uba Sani

Google search engine

Wasu da ake kyautata zaton ‘yan bindiga ne sun kona masara a gonaki shida a kauyen Kwaga da Unguwar Zako da ke karamar hukumar Birnin Gwari a jihar Kaduna.

Mutanen garin, musamman ma masu gonakin da abin ya shafa, sun shiga cikin firgici, inda suka koka da asarar da harin ya janyo musu a gonaki.

An bayyana cewa lamarin ya faru ne a daren Lahadi inda ‘yan bindigar suka far wa gonakin tare da kona duk masarar da aka girbe.

Wani daga ciki masu gonakin da abin ya shafa Kabiru Halilu Kwaga,ya shaida wa Daily Trust cewa ya girbe buhunan masara sama da 160 a shekarar da ta gabata kuma ya yi fatan samun girbi mai yawa a bana, sai dai kuma maharan sun kona dukkan amfanin gonar ta sa.

Surajo Kwaga,shima wanda ya girbe buhunan masara 40 a gonarsa a shekarar da ta gabata, ya kuma yi asarar amfanin gonarsa gaba daya bisa kona ganakin nasu da ‘yan bindigar sukai.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Gwamnatin Sokoto ta kammala aikin samar da lantarki na kashin kanta na N7bn

Gwamnatin Jihar Sakkwato ta kammala aikin gina tashar samar da wutar lantarki ta mai zaman kanta, kamar yadda Kwamishinan Makamashi, Alhaji Sanusi Danfulani, ya bayyana...

Majalisar dokokin jihar Kebbi ta dakatar da shugaban karamar hukumar Fakai

Majalisar dokokin jihar Kebbi ta dakatar da shugaban karamar hukumar Fakai a jihar Kebbi da DCL Hausa ta yi rahoton zargin da ake yi masa...

Mafi Shahara