DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Gwamnatin Nijeriya za ta gina kananan tashoshin samar da lantarki a jami’o’i

-

 Gwamnatin Nijeriya ta sanar da shirin samar da sabbin kananan tashoshin samar da hasken wutar lantarki masu amfani da hasken rana a harabar manyan makarantu da asibitocin koyarwa a fadin kasar don rage tsadar wutar lantarki

Google search engine

Ministan Wutar Lantarki, Adebayo Adelabu, ya bayyana haka a lokacin da yake duba aikin Advanced Solar Microgrid a Jami’ar Abuja, wanda ya ce an kammala kashi 95 cikin 100.

Ya ce kirkirar wadannan kananan tashoshi zai taimaka sosai wajen ganin an kawo karshen tsaiko da matsalar lantarki da ake fama a wuraren 

Nijeriya dai fama da matsalar lalacewar lantarki a sakamakon yawan samun matsala da babbar tashar samar da lantarki take yi lokaci zuwa lokaci.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Sarkin Musulmi ya bukaci gwamnoni da su rika sauraron masu sukarsu

Sarkin ya bayyana haka ne a taron Gwamnonin Arewa da majalisar sarakunan gargajiya da aka gudanar a Kaduna a Litinin din nan, Sarkin Musulmi ya...

’Yan bindiga sun sake kai hari a Kano tare da yin garkuwa da mutane 11

’Yan bindiga sun sake farmakar wani kauye a jihar Kano, inda suka yi garkuwa da mutane 11 a Unguwar Tsamiya (Dabawa), da ke ƙaramar hukumar...

Mafi Shahara