DCL Hausa Radio
Kaitsaye

‘Yan bindiga sun yi garkuwa da mutane 6,tare da halaka wani manomi a Taraba

-

Gwamnan jihar Taraba Agbu Kefas

Google search engine

‘Yan bindigar dai sun halaka manomin mai suna Alhaji Mai Wanda Maibultu a gonar sa a karshen makon da ya gabata,wanda yana daya daga cikin manyan manoma a kauyen.

Daily Trust ta rawaito cewa sauran manoma shidan da aka yi garkuwa da su,suna kauyen Garbatau, da ke tsakanin tsaunuka biyu a yanki.

Wani mazaunin garin Maihula, Adamu Dauda, ​​ya shaida wa Daily Trust cewa masu garkuwa da mutanen sun nemi iyalan manoman da suka sace, inda suka nemi Naira miliyan 100 a matsayin kudin fansa.

Ya ce, ko a shekarar da ta gabata daruruwan masu garkuwa da mutane sun addabi yankin tare da yin garkuwa da manoma da dama, inda suka hana su girbin amfanin gonakinsu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Tsadar kudin haya na hana samari aure a Sokoto – Daily Trust

Mazauna Jihar Sokoto sun koka kan tashin kudin haya, suna cewa lamarin na jinkirta aure tare da jefa matasa cikin matsin tattalin arziki da barazanar...

Kotun ƙoli ta tabbatar da ikon shugaban ƙasa na ayyana dokar ta-baci

Kotun Kolin Nijeriya ta tabbatar da ikon Shugaban Kasa na ayyana dokar ta-baci a kowace jiha domin hana tabarbarewar doka da oda. A hukuncin da ya...

Mafi Shahara