DCL Hausa Radio
Kaitsaye

‘Yan bindiga sun halaka mutum biyar tare da kona shaguna a Zamfara

-

 

Wasu ‘yan bindiga da suka kai hari a kauyen Dayau na karamar hukumar Kaura Namoda a jihar Zamfara sun yi ajalin mutam biyar tare da kona wasu gidaje da shaguna da rumbun ajiyar abinci da dama a kauyen. 

Wani mazaunin garin mai suna Shamsu, ya shaida wa jaridar Premium times cewa ‘yan bindigar sun shafe kusan sa’o’i bakwai suna cin karen su ba babba ka.

Ya kara da cewa yan bindigar sun shigo garin ne ta hanyar Kungurki a kan babura, amma ‘yan banga da jami’an tsaron al’umma sun shafe sama da sa’a day sun na arangama kafin yan yan bindigar su gudu.

Mutumin ya ce bayan sun sake dawowa ne suka shammaci jami’an, inda wasu suka riƙa harbin mai uwa da wabi wasu kuma suka kona gidaje da shaguna.

Duk kokarin da Premium Times ta yi na jin ta bakin jami’in yada labarai na rundunar yan sandan jihar Zamfara hakan ya ci tura.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

An saka ranar da za a fitar da sakamakon binciken zargin alaka da muggan kwayoyi da ya hada da Shugaba Tinubu na Nijeriya

An saka ranar da za a fitar da sakamakon binciken zargin alaka da muggan kwayoyi da ya hada da Shugaba Tinubu na Nijeriya. Ana dai...

Za mu iya cin zabenmu ko babu ku, kalaman Elrufa’i ga gwamnonin Nijeriya

  Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya bayyana cewa sabuwar kawancen jam’iyyu adawa na da karfin da zai kayar da Shugaba Bola Ahmed Tinubu...

Mafi Shahara