DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Kotu ta dakatar da hukumar tace fina-finai ta Kano daga tuhumar Rarara

-

Google search engine

Wata babbar kotun tarayya da ke Kano ta dakatar da hukumar tace fina-finai ta jahar Kano daga tuhumar mawaki Rarara kan zargin da take mishi na laifin sakin waka ba tare da ta sahale masa ba.

Jami’in yada labarai na hukumar Abdullahi Sani Sulaiman ya tabbatar da cewa kotun ta kuma dakatar da hukumar daga daukar wani mataki har sai an kammala sauraren karar da ya shigar a gabanta.

Idan ba a manta ba tun a makon da ya gabata ne hukumar tace fina-finai ta jahar Kano karkashin jagorancin Abba El-Mustapha ta shigar da mawakin kara a wata kotu da ke jahar bisa zargin sa da laifin yin gaban kansa wajen yin waka tare da sakinta ba tare da kaiwa hukumar ta tantance ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Kashi 8 cikin 100 na ‘yan Nijeriya ne kawai ke iya wanke hannu yadda ya kamata a cewar UNICEF

Asusun tallafawa kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya ce kaso 92 cikin 100 na 'yan Nijeriya ba sa iya wanke hannu yadda ya...

Majalisar wakilan Nijeriya ta gayyaci Gwamnan babban bankin kasar CBN kan wasu cajin kudade da bankuna ke yi wa al’umma

Majalisar wakilan Nijeriya ta gayyaci Gwamnan babban bankin CBN, Olayemi Cardoso, tare da shugabannin manyan bankuna domin bayyana dalilin cajin kudade ba tare da daliliba...

Mafi Shahara