DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Tabbas akwai yunwa a Nijeriya amma sauki na zuwa – Shugaba Tinubu

-

Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya ce gwamnatinsa ta mayarda hankali wajen saka jari a bangaren noma da kiwo domin magance rikicin manoma da makiyaya da kuma bunkasa tattalin arziki.
Shugaban wanda ke jawabi a birnin Rio de Janeiro na kasar Brazil, ya kuma jaddada cewa akwai matsalar yunwa a kasar, sai dai gwamnatin sa na kokarin ganin abubuwa sun daidaita.
Tinubu ya fadi haka ne a yayin da yake sanya hannu ga wata yarjejeniyar saka hannun jarin dala biliyan 2.5 da kamfanin JBS S.A, daya daga cikin manyan kamfunnan da ke sarrafa nama a fadin duniya.
Ya ce wannan yarjejeniya za ta magance matsalar rikici tsakanin manoma da makiyaya da ta jima tana damun al’umma a wannan nahiya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Buhari mutum ne mai girmama al’adu da masarautu – Sarkin Musulmi

Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar, ya shiga sahun wadanda ke jimamin rasuwar tsohon Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, wanda ya rasu a wani asibiti a...

An rufe ofishin jakadancin Amurka na Abuja da Legas don jimamin rasuwat Buhari

Ofishin jakadancin Amurka da ke Abuja da kuma na Legas za su kasance a rufe a ranar Talata, 15 ga Yuli, 2025, domin girmamawa da...

Mafi Shahara