DCL Hausa Radio
Kaitsaye

An hallaka mutane 30 a wasu kauyukan jihar Benue

-

A kalla mutum 30 ne aka hallaka a wasu kauyukka dake kananan hukumomin Kastina-Ala and Logona jihar Benue.
Mazauna yankunan sun shaidawa jaridar Dailytrust cewa lamarin ya faru ne a ranar Lahadi da kuma safiyar Litinin.
Wani basaraken yankin ya ce wasu mayaka aƙalla 300 wadanda ake zargin ba a Nijeriya suke ba, suka kai wannan hari.
Ya ce a lokacin da suka zo jami’an tsaro sun yi iya kokarin su amma an ci ƙarfin su, sai da su ka samu dauki daga jirgin yaki kafin mayakan su arce, bayan kashe mutum 20.
Hakama wani harin da wasu makiyaya suka kai a karamar hukumar Kastina-Ala ya haddasa mutuwar mutane 10.
Jami’ar yada labarai ta rundunar ‘yan sandan jihar Catherine Anene ta tabbatar da faruwar harin karamar hukumar Logo, sai dai ta ce mutum 5 aka tabbatar da mutuwar su zuwan yanzu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Wasu lauyoyi biyu daga Tanzania sun yi kara a gaban kotu suna kalubalantar zaɓen 2025 da aka gudanar a kasar

Wasu lauyoyi biyu a Tanzania, Tito Magoti da Bob Wangwe, sun kai ƙasar Tanzania gaban Kotun Gabashin Afirka kan zaɓen da aka gudanar a ranar...

Za mu karbi Peter Obi hannu biyu a jam’iyyar LP idan bai samu takara a ADC ba – Datti Baba Ahmed

Tsohon ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour Party LP,Yusuf Datti Baba-Ahmed, ya bayyana cewa Peter Obi zai samu tarba a LP idan har...

Mafi Shahara