DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Gwamna Zulum na jihar Borno ya kaddamar da raba tallafin tireloli 100 na abinci daga Shugaba Tinubu

-

Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya fara rabon tireloli 100 na kayan abinci da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ba wa mazauna Jihar Borno. An fara rabon kayan abincin, wanda ya kunshi masara, gero, da dawa, ga gidajen da suka fi bukata a Gamboru, Ngala, da wasu al’ummomi da aka kebe saboda mamakon ruwa da ambaliyar da suka shafe watanni hudu.
Da yake magana yayin kaddamar da rabon kayan, Gwamna Zulum ya jaddada muhimmancin tallafin wajen rage wahalhalun da al’ummar suka fuskanta, sannan ya gode wa Shugaba Tinubu da hukumomin tarayya da suka bada gudummawa. Haka kuma, ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta bayar da karin tireloli 100 na shinkafa domin tallafa wa wadanda ambaliyar ruwa ta shafa a Maiduguri.
Zulum ya bayyana cewa gwamnatinsa tana ci gaba da sauya matsaya daga rabon kayan abinci zuwa samar da hanyoyin dogaro da kai, ciki har da kafa tsarin ban ruwa domin noma na tsawon shekara a cikin al’ummomin da aka sake tsugunar da su, musamman a Ngala.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Shugaba Bola Ahmad Tinubu ya yi ganawar sirri da sabbin hafsoshin tsaro a Abuja

Taron, wanda ya gudana kwanaki uku bayan sanar da sabbin nade-naden, shi ne karo na farko da shugaban kasa ya gana da manyan hafsoshin rundunonin...

Paul Biya ya yi wa masu zanga-zangar sakamakon zabe shagube a Kamaru

Shugaban ƙasar Kamaru, Paul Biya, ya yi shagube ga rikicin siyasar da ke faruwa bayan ayyana shi a matsayin wanda ya lashe sakamakon zaɓen shugaban...

Mafi Shahara