DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Ma’aunin tattalin arziki GDP na Nijeriya ya karu da kashi 3.46 – hukumar kididdiga NBS

-

Hukumar kididdiga ta kasa NBS ta ce ma’aunin tattalin arzikin Nijeriya ya karu zuwa kashi 3.46 a rubu’i na uku na shekarar 2024, inda ya kai naira tiriliyan 71.1.
Wani bayani da Shugaban hukumar kididdiga ta kasa Prince Adeyemi Adeniran Adedeji, ya ce an samu ci gaba da kashi 0.92 idan aka kwatanta da rubu’i na uku na shekara ta 2023 da ma’aunin GDP ya kai kashi 2.54.
Bayanin ya kara da cewa ma’aunin a rubu’i na uku ya yi sama da kashi 0.27 idan aka kwatanta da rubu’i na biyu na wannan shekara ta 2024.
Wannan ci gaban da aka samu, hukumar kididdiga NBS ta alakanta shi da ci gaban da aka samu fannin noma da kasuwanci da sadarwa da kuma harkar gidaje.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Manyan Arewa za su tattauna yadda za a shawo kan matsalar tsaro a yankin

An shirya gudanar da babban taron tsaro a Birnin Kebbi, babban birnin jihar Kebbi, a ranar Litinin, 10 ga Nuwamba, 2025, domin tattauna hanyoyin magance...

Gwamnan Neja ya sallami shugaban hukumar SUBEB daga aiki

Gwamnan Jihar Neja, Mohammed Umaru Bago, ya kori shugaban hukumar ilimin firamare ta Jiha (SUBEB), Muhammad Baba Ibrahim, tare da dukkan mambobin dindindin na hukumar. Sanarwar...

Mafi Shahara