DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Gwamnatin Nijeriya na bin diddigin shafukan sada zumunta na ‘yan bindiga

-

Gwamnatin tarayya ta ce tana sane da yadda shafukan ‘yan ta’adda ke kara bazuwa a kafafen sada zumunta na zamani a cikin ‘yan kwanakinnan.
Wannan na zuwa ne yayin da ayyukan ‘yan bindiga ke kara karfi a shafukan sada zumunta musamman Tiktok, inda su ke nuna bindiogogi da kuma kudade zube birjik tare da yin barazanar cewa sun fi karfin gwamnati.
A wata hira da jaridar Punch, kodinetan cibiyar yaki Da ta’addanci da ke karkashin ofishin mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Maj. Gen. Adamu Laka, ya ce gwamnati na aiki tukuru domin ganin ta yaki ‘yan ta’addan ta wannan hanyar da suka É“ullo da ita.
Kodinetan ya kira ‘yan bindigar matsorata inda kalubalance su da su fito a yi gaba da gaba da jami’an tsaro ba wai labewa suna barazana ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Buhari mutum ne mai girmama al’adu da masarautu – Sarkin Musulmi

Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar, ya shiga sahun wadanda ke jimamin rasuwar tsohon Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, wanda ya rasu a wani asibiti a...

An rufe ofishin jakadancin Amurka na Abuja da Legas don jimamin rasuwat Buhari

Ofishin jakadancin Amurka da ke Abuja da kuma na Legas za su kasance a rufe a ranar Talata, 15 ga Yuli, 2025, domin girmamawa da...

Mafi Shahara