DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Za a dakatar da daliban da ke tsangwamar abokan karatunsu – Gwamnatin Nijeriya

-

Ma’aikatar ilimi ta tarayya ta yi gargadin cewa duk dalibin da aka samu da laifin cin zarafin da ya kai ga taba lafiyar abokan karatunsu, za a dakatar da shi daga kwalejojin tarayya har sai yadda hali yayi.
Wata takardar umurni da babban sakataren ma’aikatar, Nasir Gwarzo, ya sanyawa hannu ta ce ba za su zuba ido dalibai na raunata junansu ba a cikin makarantu.
Sanarwar ta ce ko a ranar 7 ga watan Nuwamba, gwamnatin tarayya ta bada umurnin dakatar da wasu dalibai 13 na tsawon makonni 6 a jihar Enugu har sai an gudanar da bincike kan zargin da ake musu na tsangwamar abokan karatunsu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Rashin tabbas da matsalolin tsaro na barazana ga burin ECOWAS na 2050 – Shugaban ECOWAS, Touray

Shugaban kungiyar ECOWAS, Omar Touray, ya ce rashin tabbas a duniya, matsalolin tsaro da matsin tattalin arziki na hana kungiyar cimma burinta na Vision 2050,...

An yi ajalin wata mace mai juna biyu da wani karamin yaro a cikin birnin Kano

Al’ummar Sheka Sabuwar Gandu a karamar hukumar Kano Municipal sun shiga firgici a daren Asabar bayan wasu da ba a san ko su waye ba...

Mafi Shahara