DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Ciwon suga ya yi sanadin rasa rayukan sama da mutane 55,000 wannan shekarar a Nijeriya

-

Google search engine
Kwararre kan ciwon suga da ake kira Diabetes a turance, Farfesa Olufemi Fasanmade na asibitin koyarwa ta jami’ar jihar Lagos ya ce sama da mutane 55, 000 ne su ka mutu sanadiyar cutar a wannan shekara.
Ya bayyana hakan ne a yayin da ‘yan jarida ta yanar gizo kan cutar ‘diabetes’ suke yi masa tambayoyi, wanda kamfanin magani na Novo Nordisk ya shirya.
Farfesa Fasanmade ya ce a shekara ta 2021 mutane 48,375 suka mutu, a shekara ta 2022 kusan mutane 50,000 suka mutu yayinda a shekara ta 2023 kusan mutane 53,000 su ka mutu sanadiyar cutar suga.
A cewar kwararren daga cikin mutum miliyan 24 da ke fama da cutar a Afrika, mutum miliyan 4 daga Nijeriya suka fito kuma ana hasashen cewa yawan su zai karu nan da shekaru 20.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

PDP ta dage tantance ‘yan takara na babban taronta na kasa

Dagewar ta zo ne ’yan sa’o’i bayan tsohon gwamnan Jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido, ya ayyana shirinsa na takarar shugabancin jam’iyyar, duk da cewa wasu...

Ina matukar tausayin mazaje masu mata daya, in ji Sanata Ned Nwoko

Ina matukar tausayin mazaje masu mata daya, akwai nutsuwa tattare da auren mace fiye da daya, in ji wani Sanata daga kudancin Nijeriya Sanata Ned Nwoko...

Mafi Shahara