DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Wasu ‘yan bindiga sun saduda, sun mika wuya ga gwamnan jihar Kaduna

-

Gwamnan jihar Kaduna Sanata Uba Sani ya ce gwamnatinsa za ta kwatanta yi wa kowa adalci duk domin a samu zaman lafiya mai dorewa a cikin al’umma.

Gwamnan ya yi wannan furucin ne a Birnin Gwari na jihar a lokacin da ya karbi kason farko na ‘ysn ta’addar da suka tuba suka rungumi sulhu a jihar.
Kazalika, Gwamnan ya ma umurci da a Bude kasuwar shanu ta Birnin Gwari da aka rufe shekaru 10 da suka gabata saboda dalilai na tsaro.
Sanata Uba Sani ya ce jihar na zama da wasu hukumomin gwamnatin tarayya don tattaunawa da ‘yan ta’adda da nufin su ajiye makamansu a dawo da zaman lafiya yadda ys dace.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Gwamna Abba K. Yusuf ya amince a biya tsofaffin Kansilolin gwamnatin Ganduje sama da 3000 kudin ritayarsu

Gwamna Abba K. Yusuf ya amince a biya kudin fanshon fiye da Naira biliyan 15 ga tsofaffin Kansilolin gwamnatin Ganduje sama da 3000 Wadanda abin ya...

PDP za ta tattauna da gwamnoninta kan sauya shekar da ‘ya’yanta ke yi

PDP za ta tattauna da gwamnoninta kan sauya shekar da 'ya'yanta ke yi nan da makon gobe Kwamitin gudanarwa na kasa (NWC) na jam’iyyar PDP tare da kungiyar gwamnonin...

Mafi Shahara