DCL Hausa Radio
Kaitsaye

‘Yan sanda sun yi amfani da ƙarfin da ya wuce iyaka akan masu zanga-zangar matsin rayuwa – Amnesty International

-

Kungiyar kare hakkin bil’adama ta Amnesty International ta ce jami’an ‘yan sandan Nijeriya sun yi amfani da ƙarfin da ya wuce iyaka akan masu zanga-zangar #EndBadGovernance.
Zanga-zangar ta faru ne daga ranar 1 zuwa 10 ga watan Augustan 2024, sanadiyar halin matsin rayuwa da ‘yan ƙasar ke fuskanta.
Wani rahoto da kungiyar Amnesty ta fitar, ya ce mutum 24 aka kashe, yayinda aka kama sama da mutum 1,200 ciki har da ƙananan yara a lokacin zanga-zangar.
Kungiyar ta bukaci a yi bincike domin hukunta waɗanda suka yi wannan aika-aikar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Majalisar dattawan Nijeriya za ta tattauna da shugaba Tinubu kan kalaman Trump

Majalisar dattawan Nijeriya ta bayyana cewa za ta gana da shugaba Tinubu da bangaren zartarwa domin tattauna batun rikicin diflomasiyya da kalaman shugaban Amurka Donald...

ECOWAS ta yi watsi da zargin Trump na halaka mabiya addinin kirista a Nijeriya

Kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka ECOWAS ta fitar da sanarwa mai dauke da watsi kan zargin cewa hare-haren ta’addanci da ke ƙaruwa a...

Mafi Shahara