DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Jirgin Max Air dauke da mataimakin Gwamnan jihar Borno da sauran fasinjoji ya yi saukar gaggawa

-

Mataimakin gwamnan jihar Borno, Umar Kadafur, da wasu fasinjoji sama da 100 sun tsallake rijiya da baya yayin da jirgin Max Air ya yi saukar gaggawa jim kadan da tashinsa daga filin jirgin saman Maiduguri. 
Jirgin da ke kan hanyarsa ta zuwa Abuja daga Maiduguri ya yi saukar gaggawa da misalin karfe 7 na daren ranar Laraba, bayan da wani tsuntsu ya shiga gabansa. 
Matukin jirgin da masu taimaka masa sun yi nasarar saukar gaggawa a filin jirgin Maiduguri, domin kaucewa kamawar jirgin da wuta. 
Wani ma’aikacin Max Air da ya nemi a sakaya sunansa ya tabbatar da faruwar lamarin a safiyar ranar Alhamis.
Jirgin a cewar jaridar Daily Trust ya bar birnin Maiduguri zuwa Abuja, amma ya ala-tilas ya koma filin jirgin Muhammad Buhari na Maiduguri jihar Borno

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Gwamnan Bauchi ya sanya hannu kan dokar kirkirar sabbin masarautu 13 a fadin jihar

Gwamnan Bauchi Bala Muhammad ya sanya hannu kan dokar kirkirar sabbin masarautu 13 a fadin jihar. Daily Trust ta ruwaito cewa a lokacin da yake sanya...

Kenya da Senegal sun kulla yarjejeniyar shige da fice ba tare da biza ba

Gwamnatocin Kenya da Senegal sun bai wa juna damar shige da fice ga 'yan kasashensu ba tare da biza ba na tsawon kwanaki 90. DW Africa...

Mafi Shahara