DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Amnesty International ta yi zargin mutuwar mutune 10,000 dake tsare a hannun sojojin Nijeriya

-

 

Kungiyar kare hakkin bil’adama ta Amnesty International ta yi zargin cewa mutane 10,000 sun mutu tsare a hannun sojojin Nijeriya tun bayan da yaki ya barke a yankin arewa maso gabas.
Daraktan hukumar a Nijeriya Isa Sanusi ne ya bayyana hakan, a yayin wata ganawa da manema labarai a birnin Maiduguri.
A cewarsa, jami’an sojin Nijeriya sun saba dokoki harbi da kuma tsare al’umma ba bisa ka’ida ba, lokacin da suke yaki da kungiyar ‘yan ta’addan da ta addabi yankin tafkin Chadi.
Amnesty International kuma ta zargi gwamnatin Nijeriya da kasa gudanar da bincike domin hukunta wadanda ake zargi da aikata wannan aika-aikar kamar yadda dokokin kasa da kasa suka tanada.
Sai dai a martanin da ta mayar, hedikwatar tsaron Nijeriya, a cikin wata sanarwa da Kakakinta Major General Edward Buba ya fitar, ta musanta zarge-zargen na Amnesty International.

Google search engine

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Jam’iyyar ADC ta fara rajista da tantance mambobi na kwanaki 90 a fadin Nijeriya

Jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) ta fara shirin rajista, tantancewa da kuma jawo sabbin mambobi na tsawon kwanaki 90 a fadin Nijeriya, domin karfafa jam’iyyar...

Ya kamata a haramta amfani da kafafen sada zumunta ga ’yan kasa da shekara 16 a Nijeriya – Femi Falana

Babban lauya kuma SAN, Femi Falana, ya bukaci a haramta amfani da kafafen sada zumunta ga yara ’yan kasa da shekara 16 a Nijeriya, yana...

Mafi Shahara