DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Masu sana’ar ‘DJ’ sun yi zanga-zanga ga hukumar Hisbah a Katsina

-

Masu sana’ar DJ da ke nishadantar da taron mutane a lokuttan bukukuwa sun cika makil a filin taro na Kangiwa Square a jihar Katsina, inda suka yi zanga-zanga ga hukumar Hisbah ta jihar bisa dakatar da sana’ar su da ta yi na tsawon watanni 8.
Masu sana’ar sun ma roki gwamnatin jihar Katsina da ta sa baki a bar su, su ci gaba da gudanar da sana’ar su da suka ce ba su takura wa kowa kuma ba su shiga hakkin kowa. Sun kuma koka kan cewa hukumar Hisbah din ta kwace musu kayan aiki na milyoyin Nairori.
Zanga-zangar ta su, ta yi daidai da lokacin da Gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Umaru Radda ke bude aikin fadada titin Kofar Soro zuwa Kofar Guga cikin kwaryar birnin Katsina da aka kammala kamar yadda gidan talabijin na Channels ya rawaito.
An dai ga matasan dauke kwalaye masu rubutun da ke nuna irin halin da suka ce suna ciki tun bayan dakatar musu da sana’ar da hukumar ta Hisbah ta yi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Manufofin tattalin arzikin Tinubu sun taimaka wajen samun dumbin arziki a Nijeriya – Hope Uzodimma

Gwamnan jihar Imo, Hope Uzodimma, ya ce manufofin tattalin arziƙin da shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bijiro dasu sun taimaka wajen farfaɗo da tattalin arziƙin...

Jami’ar kimiyya da fasaha ta Aliko Dangote da ke Wudil a Kano, ta kori dalibai 34 bayan an same su da laifin satar...

Jami’ar kimiyya da fasaha ta Aliko Dangote da ke Wudil a Kano, ta kori dalibai 34 bayan an same su da laifin satar amsa a...

Mafi Shahara