DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Shugaban ƙasar Brazil Lula da Silva na ci gaba da murmurewa bayan tiyatar kwakwalwa da aka yi masa

-

Luiz Inacio Lula De Silva

An yi wa shugaban kasar Brazil Luiz Inacio Lula De Silva tiyata sakamakon taruwar jini a kwakwalwarsa sanadiyar faduwar da ya yi a baya-bayan nan.

Google search engine

A wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Instagram a ranar Talata, wani asibiti mai suna Syrian-Lebanese da ke Sao Paulo na Brazil ya tabbatar da hakan. 

A cikin sanarwar asibitin ya ce tun a daren ranar Litinin  ne aka kammala aikin ba tare da wata matsala ba, kuma yanzu haka shugaban kasar ta Brazil yana cikin yanayi mai kyau inda yake ci gaba da samun sauki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Tinubu ya umurci sabbin hafsoshin tsaro da su murƙushe duk wata barazanar tsaro

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya umurci sabbin hafsoshin tsaron da su tashi tsaye wajen murƙushe duk wata barazanar tsaro da ke tasowa a sassan...

Sojojin da ake tsare da su bisa zargin juyin mulki a Nijeriya sun kai 42 a wani binciken jaridar Daily Trust

Yawan sojojin da ake tsare da su bisa zargin yunƙurin juyin mulki ya ƙaru zuwa 42, kamar yadda majiyoyi daga cikin rundunar sojin suka tabbatar...

Mafi Shahara