Tsohon sakataren gwamnatin tarayya Babachir Lawal, ya bayyana cewa jihohin arewacin Nijeriya za su shiga da yawa idan aka sanya haraji kan kayan amfanin gona da dabbobi da suke samarwa.
A cikin wani bayani da da fitar kan dokar harajin Tinubu da ake cece-kuce a kanta, Babachir Lawal ya ce wadanda su ka goyi bayan dokar suna tunanin cewa saboda zaman ‘yan arewa cima kwance ne yasa suke jayayya da dokar.
Sai dai ya yi Allah wadai da masu wannan tunanin musamman ‘yan kudu, inda ya ce mafi yawan kayan abincin da ake kaiwa Kudu daga Arewa ake samar da shi kuma idan aka sanya musu haraji jihohin arewa za su samu kudin da ake baiwa jihohin Kudu bayan an sarrafa kayan gona.