Yahaya Bello
Wata babbar kotun tarayya dake zamanta a Abuja, ta amince da bayar da belin tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, kan kudi Naira Miliyan 500 tare da mutane biyu da za su tsaya masa.
Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya musanta tuhumar da ake masa na karkatar da naira biliyan 80 da hukumar yaki da yi wa tattalin arzikin zagon kasa ta EFCC ta yi masa.
An gurfanar da Bello a gaban mai shari’a Emeka Nwite na babbar kotun tarayya Abuja a kan tuhume-tuhume 19 na badakalar kudade.




