DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Shugaba Tinubu ya amince da sufuri a jiragen kasa kyauta ga ‘yan Nijeriya

-

A kokarin saukaka zirga-zirga a lokacin bukukuwan Kirsimeti, Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya amince da sufurin jiragen kasa kyauta ga ‘yan kasar daga ranar 20 ga watan Disamban 2024 zuwa 5 ga watan Janairu 2025.
Ministan yada labarai na tarayya Mohammed Idris, shi ne ya bayyana hakan a Abuja, bayan taron majalisar zartarwa na ƙasar.
Muhammad Idris ya ce wannan zai saukaka wa ‘yan Nijeriya musamman marasa karfi a bangaren kashe kudaden sufuri.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Tankiya tsakanin Nijer da Benin ta sa kasashen rufe ofisoshin jakadancin juna

Kasashen Benin da Niger sun kori jami’an diflomasiyyar juna a wani mataki na ramuwar gayya, bayan shafe kusan shekara biyu ana takun-saka a tsakaninsu, a...

‘Yan bindiga sun yi ajalin mutane fiye da 30 a jihar Neja

Aƙalla mutane 30, ciki har da mata, sun rasu bayan da ‘yan bindiga suka kai hari Kasuwan Daji da ke ƙauyen Demo, Borgu LGA a...

Mafi Shahara