DCL Hausa Radio
Kaitsaye

‘Yan majalisar wakilai za su kai wa Shugaba Tinubu tallafin N704.91m don a raba wa talakawa

-

A ranar 31 ga watan Disamba 2023, ajalisar wakilan Najeriya za ta gabatar da tallafin naira milyan N704.91 ga Shugaba Bola Tinubu domin amfani da kudin wajen ragewa talakawa radadin cire tallafin man fetur.
Idan za a iya tunawa, ranar 18 ga watan Yuli majalisar ta amince a ware kashi 50 da ga dubu 600 na albashin kowane dan majalisa har tsawon watanni 6 domin magance matsalolin da talakawa ke fuskanta.
A zaman majalisar na yau, Tajuddeen Abbas, Kakakin majalisar ya ce zai jagoranci tawagar da za ta mikawa shugaban kasa kuɗaɗen kamar yadda a ka yi alkawari.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Mutane 7 sun hadu da ajalinsu sakamakon harsaniya tsakanin ‘yan bindiga da masu hakar ma’adanai a Birnin Gwari jihar Kaduna

Akalla mutane bakwai ne suka rasa rayukansu bayan hatsaniya ya barke tsakanin wasu da ake zargin ’yan bindiga da masu hakar ma’adanai ba bisa ka’ida...

Barayin daji sun kai sabon samame a wani kauyen karamar hukumar Kusada, jihar Katsina

Bayanai daga kauyen Tittike da ke mazabar Boko a karamar hukumar hukumar Kusada jihar Katsina na cewa barayin daji sun kai hari inda suka yi...

Mafi Shahara