DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Ma’aikatan gwamnatin tarayya sun yi bikin Kirsimeti wayam ba tare da albashin watan Disamba ba – Jaridar Punch

-

Ma’aikatan gwamnatin Nijeriya na sun fara shagulgulan buki Kirsimeti a wani yanayi na Allah Ka wadata mu, saboda tsaikon biyan albashin watan Disamban 2025.
Binciken jaridar Punch ya nuna cewa ko albashin watan Nuwamba wasu ma’aikatan ba su sake shi ba sai a mako na biyu na watan Disamba, abinda da dama daga cikin ma’aikatan ke kokawa.
Wasu majiyoyi sun ce matsalar ta faru ne a ofishin akanta na kasa yayinda wasu su ka alakanta tsaikon da aka samu da sauyin tsarin biyan albashin da aka yi da wata sabuwar manhaja.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

SERAP ta soki gwamnatin Tinubu game da karin fasfo

Ƙungiyar SERAP mai fafutikar tabbatar da adalci da shugabanci nagari ta bukaci gwamnatin Nijeriya da ta soke ƙarin kuɗin fasfo da hukumar shige da fice...

ADC ta nesanta kanta da Nasiru El-Rufa’i bayan taron jam’iyyar da aka yi tashin hankali a Kaduna

Rikicin siyasa na ƙara kamari a jihar Kaduna bayan jam’iyyar ADC ta nesanta kanta daga wani taron da aka danganta da tsohon gwamnan jihar, Nasir...

Mafi Shahara