DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Sabuwar Shekara: Tinubu ya yi alkawarin bunkasa samar da abinci da rage hauhawar farashi zuwa kashi 15 a 2025

-

Shugaban Nijeriya Bola Ahmad Tinubu ya tabbatar wa ‘yan kasar kudirin gwamnatinsa na bunƙasa samar da abinci da kuma rage hauhawar farashi zuwa kashi 15 ta hanyar bunkasa tattalin arziki a sabuwar shekarar 2025
A cikin sakon barka da sabuwar shekara da ya aike wa ‘yan Nijeriya, Shugaba Tinubu ya bayyana saukar farashin fetur da ƙaruwar kudaden ajiya na kasa da kuma farfaɗowar darajar naira, a matsayin wasu alamomin da ke nuna cewa tattalin arzikin kasar na kan hanyar ci gaba.
Shugaban ya kara da cewa kasuwar hannun jari ta kasar na kara bunkasa tare da samar da kudaden shiga haka kuma masu zuba hannun jari daga kasashen waje na ci gaba da ƙaruwa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Dalori ya karbi ragamar jagorancin jam’iyyar APC a hukumance

Shugaban riko na jam’iyyar APC, Ali Bukar Dalori, ya bukaci shugabanni da mambobin jam’iyyar da su zauna cikin hadin kai bayan murabus din tsohon shugaban...

An dakatar da jirgin Rano Air kan zargin matsalar inji – NCAA

Hukumar kula da sufurin jiragen sama ta Najeriya (NCAA) ta dakatar da wani jirgin Rano Air mai lamba 5N-BZY bayan fuskantar hatsarin gobara da matsalar...

Mafi Shahara