DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Fetur na biliyan 2 za a saka wa motocin jami’an tsaron DSS da hukumar EFCC a 2025

-

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa a Nijeriya EFCC da hukumar jami’an tsaron farin kaya DSS za su kashe naira biliyan biyu wajen saka mai ga motocinsu a shekara ta 2025, kamar yadda jaridar Punch ta gani a cikin kudurin kasafin kudi.
Kasafin naira tiriliyan 47.90 da Shugaba Bola Tinubu ya gabatar wa majalisa a Disambar bara, an ware tiriliyan 4.91 ga bangaren tsaro domin ingata ayyukan jami’an tsaro wajen yaki da ta’addanci.
Bincike ya nuna cewa an ware wa hukumar EFCC naira miliyan N808.7 domin shan mai, sai wasu N462m na ciye-ciye da tande-tande. Haka kuma hukumar DSS an ware mata naira biliyan N1.37 domin sayen fetur.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Gwamna Zulum zai ba duk dan Borno da ke hijira a Kamaru N500,000

Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya bayyana cewa gwamnatin jiharsa za ta ba kowane É—an gudun hijira É—an Borno da yake a Kamaru...

Najeriya da Saudiyya sun rattaba hannu kan yarjejeniyar tsaro

Najeriya da Masarautar Saudiyya sun kulla sabuwar yarjejeniya ta shekaru biyar domin ƙarfafa haɗin gwiwar tsaro da dangantakar soja tsakanin kasashen biyu. A cewar wata sanarwa...

Mafi Shahara