Ma’aikatan CBN 1000 da su ka bar aiki ba tursasa su aka yi ba – Gwamnan babban bankin Nijeriya

-

Babban bankin Nijeriya ya yi karin haske cewa, ma’aikata 1000 da su ka bar aiki a shekarar 2024 ba tursasa su aka yi ba don su ajiye aiki.
Gwamnan CBN Olayemi Cardoso, ya sanar da hakan a gaban kwamitin bincike na majalisar wakilai da ke bincike akan dalilin barin aikin ma’aikatan da kuma yadda aka amince da biyansu naira biliyan 50 a matsayin hakkinsu na barin aiki.
Cardoso ya ce duk wadanda abin ya shafa sun ajiye aiki ne bisa radin kansu, karkashin wani shiri na biyan ma’aikata duk hakkokinsu idan su ka ajiye aiki da wuri.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Mun ji takaicin ficewar gwamna Sheriff Oborevwori na jihar Delta daga PDP zuwa APC- Umar Damagum

Shugaban ruko na jam’iyyar PDP na ƙasa, Umar Damagum, ya bayyana ficewar Gwamna Sheriff Oborevwori na Jihar Delta, tare da wasu manyan jiga-jigan jam’iyyar zuwa...

Talauci zai karu a Najeriya nan da 2027 – Bankin Duniya

Bankin Duniya ya bayyana cewa yawan mutanen Najeriya da ke fama da talauci zai karu nan da shekarar 2027, duk da kasancewar kasar na daga...

Mafi Shahara