DCL Hausa Radio
Kaitsaye

An sako wasu mata ‘yan Nijeriya bayan shafe watanni 10 tsare a Saudiyya bisa zargin safarar kwayoyi

-

Ma’aikatar harkokin wajen Nijeriya ta sanar da sakin wasu mata uku ‘yan Nijeriya da aka gurfanar a kasar Saudiyya bisa zargin safarar miyagun kwayoyi, bayan sun shafe watanni 10 a tsare gidan kaso.
Sanarwar da mai magana da yawun ma’aikatar Kimiebi Ebienfa ya fitar, ta tabbatar da sako matan bayan an bi hanyoyin diflomasiyya.
A watan Maris na 2024 ne aka damke Hadiza Abba, da Fatima Umate Malah, da kuma Fatima Kannai Gamboil a filin jirgin saman kasa da kasa na Yarima Mohammad bin Abdulaziz da ke birnin Madinah.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Ba gasa muke yi da kamfanin NNPCL ba – Dangote

Shugaban Rukunin kamfanonin Dangote, alhaji Aliko Dangote, ya bayyana cewa matatar man fetur dinsa ba ta yin gasa da Kamfanin man Fetur na Nijeriya, wato...

Hukumomin mulkin sojan Nijar sun kama wasu ‘yan jarida uku na Radio Sahara da ke jihar Agadez

Rahotanni daga gidan Radio Sahara Fm da ke jihar Agadez sun tabbatar da kama wasu 'yan jaridar gidan radiyon guda uku da suka hada da...

Mafi Shahara