DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Tsohon kwamishinan raya karkara da ci gaban al’umma, da gwamnan Kano ya cire Abbas Sani Abbas, ya fice daga jam’iyyar NNPP zuwa jam’iyyar APC mai adawa a jihar

-

Abdullahi Abbas/Abbas Sani Abbas/Barau Jibrin

 

Google search engine

Abbas Sani Abbas, wanda Gwamna Abba Kabir Yusuf ya sallama kwanakin baya tare da wasu kwamishinoni biyar, mataimakin shugaban majalisar dattawa Barau Jibrin ya karbe shi zuwa APC.

Mataimakin shugaban majalisar dattawan Nijeriya Barau Jibrin tare da wasu jiga jigai a APC ciki harda shugaban jam’iyyar na Kano Abdullahi Abbas ne suka karbe shi inda suka yi masa maraba zuwa jam’iyyar su ta APC.

Barau ya ce karbar guda daga cikin jiga jigan jam’iyyar ta NNPP ba karamin nasara bace a gare su inda ya ce wannan ne zai kara bada dama domin samun makoma mai kyau ga al’ummar jihar Kano da   Nijeriya baki daya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Gwamnan Kano ya rattaba hannu kan bukatar samar da kwalejin Polytechnic a Gaya

Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya sanya hannu kan dokar kafa kwalejin kimiyya da fasaha "Gaya Polytechnic" a wani mataki na fadada damar samun ilimin...

Ma’aikatan majalisa sun rufe majalisar dokokin jihar Bauchi sakamakon tsunduma yajin aiki 

Shugaban ƙungiyar ma’aikatan majalisun jihohi ta Nijeriya (PASAN) a jihar Bauchi Adamu Yusuf ne ya sanar da hakan ranar Juma’a, bisa bin umarnin shugabancin ƙungiyar...

Mafi Shahara