Tsohon kwamishinan raya karkara da ci gaban al’umma, da gwamnan Kano ya cire Abbas Sani Abbas, ya fice daga jam’iyyar NNPP zuwa jam’iyyar APC mai adawa a jihar

-

Abdullahi Abbas/Abbas Sani Abbas/Barau Jibrin

 

Abbas Sani Abbas, wanda Gwamna Abba Kabir Yusuf ya sallama kwanakin baya tare da wasu kwamishinoni biyar, mataimakin shugaban majalisar dattawa Barau Jibrin ya karbe shi zuwa APC.

Mataimakin shugaban majalisar dattawan Nijeriya Barau Jibrin tare da wasu jiga jigai a APC ciki harda shugaban jam’iyyar na Kano Abdullahi Abbas ne suka karbe shi inda suka yi masa maraba zuwa jam’iyyar su ta APC.

Barau ya ce karbar guda daga cikin jiga jigan jam’iyyar ta NNPP ba karamin nasara bace a gare su inda ya ce wannan ne zai kara bada dama domin samun makoma mai kyau ga al’ummar jihar Kano da   Nijeriya baki daya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Mun ji takaicin ficewar gwamna Sheriff Oborevwori na jihar Delta daga PDP zuwa APC- Umar Damagum

Shugaban ruko na jam’iyyar PDP na ƙasa, Umar Damagum, ya bayyana ficewar Gwamna Sheriff Oborevwori na Jihar Delta, tare da wasu manyan jiga-jigan jam’iyyar zuwa...

Talauci zai karu a Najeriya nan da 2027 – Bankin Duniya

Bankin Duniya ya bayyana cewa yawan mutanen Najeriya da ke fama da talauci zai karu nan da shekarar 2027, duk da kasancewar kasar na daga...

Mafi Shahara