DCL Hausa Radio
Kaitsaye

‘Yan sanda a Kaduna sun kama mutum 2 da ake zargin masu garkuwa da mutane ne, da ‘yan fashi da makami 4

-

 

‘Yan sanda

Google search engine

‘Yan sanda a jihar Kaduna sun kama wasu mutane biyu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne da kuma wasu ‘yan fashi da makami guda hudu a yankin Samaru da ke karamar hukumar Zariya.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar, Mansir Hassan ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar.

Ya baiyana cewa an kama wadanda ake zargin ne bisa sahihan bayanan sirri da aka samu.

Mansir Hassan ya ce bayan samun bayanan sirrin da jami’an ‘yan sandan da ke Samaru a Zariya su ka yi, ba tare da ɓata lokaci ba suka kaddamar da wani samame a yankin Zango da Hayin- Jarumai da ke Samaru a Zariya, lamarin da ya kai ga kama mutane hudu da ake zargi da aikata fashi da makami.   

Wadanda ake zargin sun haɗa da Abubakar Alkamu, Ahmed Isah, Hassan Isah da Umar Abubakar.

Rundunar ‘yan sandan ta ce a wani bincike da ta gudanar a gidan Hassan Isah, jami’an sun gano wata wuka da ake zargin ana amfani da ita wajen aikata miyagun laifuka na.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Ka fito ka bayyana wa ‘yan Nijeriya hakikanin dalilin da ya sa ka canza hafsoshin tsaro – Bukatar ADC ga shugaba Tinubu

Jam’iyyar ADC ta bukaci shugaban Nijeriya, Bola Tinubu ya bayyana gaskiya ga ’yan Nijeriya kan ainihin dalilan da suka sa aka yi gaggawar sauya shugabannin...

Gwamnan jihar Bauchi Bala Muhammad ya nada yayansa a matsayin Sarkin Duguri

Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya naɗa yayansa, Alhaji Adamu Mohammed, a matsayin sarkin sabon masarautar Duguri da aka ƙirƙira a jihar. Sakataren gwamnatin Jiha, Aminu...

Mafi Shahara