DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Sojoji na dab da yi wa Bello Turji ‘Ƙofar Raggo’ – Rundunar sojin Nijeriya

-

Rundunar sojin Najeriya ta ce nan ba dadewa ba ƙasurgumin dan ta’adda Bello Turji zai zo hannu.
Jami’in yada labaran rundunar ta operation Fansar Yamma Laftanal Kanal Abdullahi ne ya bayyana haka a lokacin da yake gabatar da makaman da rundunar ta ƙwace daga ‘yan bindiga a karamar hukumar Kaura -Namoda dake jihar Zamfara.
Abubakar ya ce Turji na cigaba da wasan buya tsakaninsa da rundunar, sai dai ya tabbatar wa da ‘yan Nijeriya rundunar za ta kamo shi.
Jami’in ya yaba tare da godewa al’umma bisa hadin kai da bayanan sirri da suke bai wa rundunar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Tinubu ya fasa bai wa Abdullahi Ramat mukamin shugabancin hukumar NERC?

A wata wasika da shugaban Nijeriyar ya aike wa Majalisar Dattawa a cikin makon nan, Tinubu ya bukaci sanatoci su amince masa ya nada Aisha...

Hukumar KAROTA ta mika wa HISBAH motocin barasar da ta kama a Kano

Hukumar Kula da Harkokin sufiri ta Jihar Kano wato KAROTA ta mika manyan motoci guda uku da ke ɗauke da kwalaben giya na miliyoyin naira...

Mafi Shahara