DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Ba lallai Nijeriya ta iya cike kujerun aikin hajjin da Saudiyya ta ware mata na hajjin 2025, saboda cikar wa’adin biyan kudin kujera a ranar 31 ga watan Junairu – binciken Daily Trust

-

 

NAHCON

Google search engine

Yayin da wa’adin hukumar alhazan Nijeriya NAHCON na kammala biyan kudin aikin hajji ke cika a yau 31 ga watan Janairu, rahotanni sun nuna cewa akwai yiwuwar kara wa’adin kasancewar zuwa yanzu alhazai dubu 51,447 ne kacal suka kammala biyan kudinsu, duk da cewa Nijeriya ta samu gurbin mutum 95,000.

Sai dai wasu jami’an hukumar sun danganta rashin biyan kudin da tsadar kudin aikin hajji da kuma karancin lokacin biyan kudin da aka sanya, kamar yadda Dailytrust ta ruwaito.

Farashin kudin aikin hajjin bana ya kai naira milyan N8.3m zuwa milyan N8.7m a sassan Nijeriya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Har yanzu bamu kammala bincike ba shiyasa bamu gurfanar da El-rufa’i a gaban kotu ba – EFCC

Hukumar EFCC, mai yaki a cin hanci da rashawa a Nijeriya ta bayyana dalilin da ya sa har yanzu ba ta kai tsohon gwamnan Kaduna,...

Wanene sabon Shugaban Rundunar ‘Yan Sandan Nijeriya, Olatunji Disu?

AIG Olatunji Disu ya kasance gogaggen jami’i wanda aka nada don jagorantar rundunar 'yan sandan kasar a matsayin IGP na 23. A cewar fadar shugaban...

Mafi Shahara