DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Hukumar shirya jarabawar shiga jami’o’i a Nijeriya JAMB ta dage fara rejistar dalibai zuwa 3 ga watan Fabrairu

-

JAMB

Babban jami’in hukumar da ke kula da harkokin hulda da jama’a, Dr Fabian Benjamin, ya sanar da haka a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a.

Google search engine

Ya ce sauyin lokacin ya zama dole domin bai wa hukumar damar aiwatar da wasu muhimman gyare gyare ga tsarin yin rajistar.

Dr Fabian Benjamin ya kara da cewa hukumar JAMB ta gano cewa akwai wasu cibiyoyi na jarrabawa CBT da ake zargin suna amfani da kayan aikin da basu dace ba da yaudara, lamarin da ya jaddada bukatar yin bincike don kawo gyara ta hanyar kin amincewa da irin wadannan cibiyoyin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Babban layin wutar lantarkin Nijeriya National Grid ya fadi

Babban layin wutar lantarki na ƙasa ya fadi Litinin din nan, lamarin da ya jefa ’yan Nijeriya da dama cikin duhu bayan da manyan tashoshin...

‘Yan bindiga sun kai hari a wani kauye na jihar Kebbi

’Yan bindiga sun kai hari a kauyen Gebbe da ke karamar hukumar Shanga a jihar Kebbi, inda rahotanni ke nuna an rasa rayuka yayin da...

Mafi Shahara