DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Ba mu da shirin hana amfani da lasifika a masallatai – Gwamnan jihar Filato, Caleb Mutfwang

-

 

Celeb Muftwang

Google search engine

Gwamnan jihar Filato, Caleb Mutfwang, ya musanta ikirarin da ake yi cewa gwamnatinsa na shirin hana amfani da lasifika a masallatai.

Hakan ya biyo bayan yada koke a shafukan sada zumunta na neman haramta wa, wanda wani John Apollos Maton ya yi ga gwamna, kwamishinan ‘yan sanda, da kuma hukumar kare hakkin dan Adam ta kasa.

Koken dai ya haifar da cece kuce musamman a kafafen sada zumunta da na gidajen rediyon jihar.

Gwamna Mutfwang yayin da yake jawabi a yammacin ranar Juma’a a birnin Bukur, ya tabbatar wa al’ummar Musulmin jihar cewa wannan zargi ba shi da tushe balle makama, ya kuma bukace su da su yi watsi da shi.  

Ya ce gwamnati, ba ta da masaniya kan wannan batu, kuma masu yada wannan jita jita sun san ba gaskiya ba ne kuma suna kokarin kawo barna a jihar,a cewar sa ana kan binciken wadanda da ke yada wannan jita jita.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Za a iya kawo karshen matsalolin Arewa aka hada kai – Uba Sani

Gwamnan Kaduna, Uba Sani, ya ce Arewacin Nijeriya na da kwararru da hazikan ‘yan kasa da za su iya magance matsalolin ci-gaba da ake fama...

Halin kuncin da ‘yan Nijeriya ke ciki ne zai yanke wa Tinubu hukunci a zaben 2027 – NNPP

Jam’iyyun hamayya na NNPP da ADC reshen jihar Osun sun ce halin tsananin talauci da ake ciki yanzu shi ne zai yanke wa shugaban Nijeriya...

Mafi Shahara