Yaro Yaro ya zama sabon mai horar da Kano Pillars bayan dakatar da Usman Abdullahi

-

 

Yaro Yaro

Tsohon dan wasan tawagar Super Eagles da Borussia Dortmund Ahmed Garba Yaro Yaro ya zama sabon mai horar da kungiyar Kano Pillars.

Hakan ya biyo bayan dakatar da mai horar da kungiyar Usman Abdullah da mahukuntan kungiyar ta Pillars suka yi biyo bayan rashin abun azo gani da kumgiyar ke yi a bana.

Canjaras da kungiyar ta yi da Bayelsa United ya kara harzuka magoya baya dsshugabanni na tawagar sai Masu Gida, da hakan ke biyo bayan dukan kawo wuka na ci 4-1 da ta karba a hannun Ikorodu United ta Lagos a Larabar makon da ya gabata.

A Sanarwar da kungiyar ta fitar ta bakin shugaban tawagar Alhaji Ali Nayara, Yaro Yaro wanda tsohon dan wasan kungiyar ne ta Pillars zai jagoranci kungiyar a yanzu kafin kwamitin bincike da aka kafa kan Usman Abdullah ya kammala aikin sa don samun matsaya a gaba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Mun ji takaicin ficewar gwamna Sheriff Oborevwori na jihar Delta daga PDP zuwa APC- Umar Damagum

Shugaban ruko na jam’iyyar PDP na ƙasa, Umar Damagum, ya bayyana ficewar Gwamna Sheriff Oborevwori na Jihar Delta, tare da wasu manyan jiga-jigan jam’iyyar zuwa...

Talauci zai karu a Najeriya nan da 2027 – Bankin Duniya

Bankin Duniya ya bayyana cewa yawan mutanen Najeriya da ke fama da talauci zai karu nan da shekarar 2027, duk da kasancewar kasar na daga...

Mafi Shahara