DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Hukumar tace finafinai ta jihar Kano ta dakatar da daukar wani fim mai suna “Zarmalulu”

-

 

Hukumar tace fina-finai ta jihar Kano ta dakatar da wani film mai suna ‘Zarmalulu’ tare da gayyatar dukkannin wadanda suka fito a cikinsa domin jin ba’asi, biyo bayan zargin yin amfani da kalmar badala a matsayin sunan film din.
Hukumar karkashin jagorancin Alhaji Abba El-Mustapha ta ce ta karbi korafi daga wasu yan kishin jihar Kano akan wannan film din bisa zargin rashin ma’ana.
Abba El-Mustapha ya bayyana damuwarsa akan lamurin tare da bayar da umarnin dakatar da film din, haka kuma ya gayyaci dukkannin wadanda ke da ruwa da tsaki a shirin.
A cikin wata sanarwa daga jami’in hulda da jama’a na hukumar Abdullahi Sani Sulaiman da ya aike wa DCL Hausa, ta ce hukumar na da hurumin dakatar da dukkanin wani fim da ba ta gamsu da yadda aka shirya shi ba, tare da ladabtar da duk wanda ta samu da yin abin da bai kamata ba a cikin kowane fim.

Google search engine

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Shugaba Tinubu adali ne, bai fifita kowane yanki ba wajen rarraba ayyukan ci-gaba ba a Nijeriya – Gwamnatin tarayya

Gwamnatin Nijeriya ta bayyana cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu na gudanar da mulkinsa bisa gaskiya da adalci wajen rabon ayyuka, mukamai da damar ci-gaba...

Dalilin da ya sa muka maye gurbin rundunar Operation Safe Haven da Enduring Peace – Babban hafsan tsaron Nijeriya

Babban hafsan tsaron Nijeriya, Janar Christopher Musa, ya ƙaddamar da sabuwar rundunar haɗin gwiwa mai suna Operation Enduring Peace domin magance matsalar tsaro da ta...

Mafi Shahara