DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Gwamnatin Nijeriya ta musanta zargin babban jami’in Binance cewa ‘yan majalisa 3 sun nemi cin hancin $150m

-

Gwamnatin Nijeriya ta musanta zargin babban jami’in kamfanin Binance Tigran Gambaryan wanda ya shafe watanni takwas yana tsare a hannun hukumomin Nijeriya bisa zargin rashawa.
Gambaryan wanda dan kasar Amurka ne, an sake shi bayan da gwamnatin kasar ta shiga tsakani, sai dai a wani sako da ya wallafa a shafinsa na X ya zargi gwamnatin Nijeriya da tsare shi ba bisa ka’ida ba.
Ya kuma yi zargin cewa wasu ‘yan majalisa uku sun nemi ya basu cin hanci na dala miliyan 150.
A martanin gwamnatin, ta hannun ministan yada labarai Mohammed Idris, ta ayyana kalaman a matsayin yunkurin yada labaran karya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

NAHCON ta gargadi maniyyata Hajjin 2026 na Nijeriya kan yin rijista da wuri

By Fatima Aminu Dabo Hukumar jin daÉ—in alhazai ta kasa NAHCON ta sanar da jadawalin aikin Hajjin 2026, inda ta bayyana cewa 20 ga Maris, 2026...

Ana ci gaba da neman wata dattijuwa bayan kifewar kwale-kwale dauke da fasinja 11 a Sokoto

An gano gawar wani matashi mai shekara 29 da ya rasa ransa a wani hatsarin jirgin ruwa da ya afku a Jihar Sokoto.Lamarin ya faru...

Mafi Shahara