DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya haramta sanya dalibai aiki mai tsauri a cikin makarantu

-

Abba Kabir Yusuf

Gwamnan jihar Kano Abba Yusuf ya yi gargadi ga malaman makarantu da kada su umurci dalibai yin ayyuka masu tsauri a ciki ko wajen makaranta.

Google search engine

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar ga manema labarai.

Gwamnan ya jaddada cewa makarantu wajen ba da ilimi ne da jagoranci, kyautata ɗabi’a ba wajen bautar da dalibai ba.

A wata ziyarar bazata da gwamnan ya kai wata makarantar koyar da larabci da ke Kano, ya tarar da dalibai su na aiki mai wahala a cikin makarantar .

A bayyane gwamnan ya nuna rashin jin daɗi, tare da  tambayar shugaban makarantar game da sanya dalibai irin waɗannan ayyuka.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Gasar cin kofin kasashen nahiyar Afirka AFCON za ta koma duk bayan shekaru 4 – CAF

Hukumar kwallon kafa ta nahiyar Afrika CAF, ta sanar da cewa gasar cin kofin kasashen Afrika AFCON, za ta koma duk bayan shekara huɗu bayan...

Tinubu ya ziyarci jihar Borno domin bude ayyuka

Shugaba Tinubu, ya ziyarci Maiduguri, babban birnin Jihar Borno, domin ƙaddamar da manyan ayyuka da halartar bikin auren ɗan tsohon gwamnan jihar, Sanata Ali Modu...

Mafi Shahara